Home General Najeriya da Nijar da kuma Aljeriya sun cimma yarjejeniyar shimfiɗa bututun gas...

Najeriya da Nijar da kuma Aljeriya sun cimma yarjejeniyar shimfiɗa bututun gas zuwa Turai

Ƙasashen Aljeriya da Najeriya da kuma Jamhuriyar Nijar, sun ƙulla sabuwar yarjejeniya da nufin gaggauta gudanar da akin shimfiɗa bututun iskar gas mai tsawon kilomita sama da dubu 4, da zai sada ƙasashen da nahiyar Turai.

A yarjejeniyar, ƙasashen 3 sun amince su yi amfani da bututun Transmed wanda Aljeriya ke amfani da shi don bai wa Italiya makamashin gas, sai a yanzu maimakon Italiya kawai da ke cin gajiyarsa, za a riƙa tura makamashin zuwa sauran ƙasashen Turai.

Yarjejeniyar da wakilan ƙasashen uku suka rattaba wa hannu ranar Talata da ta gabata, ta fayyace adadin kuɗaɗe da tsawon lokacin da ake buƙata don aiwatar da wannan aikin, sai kuma batun biyan diyya da kuma zaɓen ƙmfanonin da za su aiwatar da wannan aiki.

Tun a shekara ta 2009 ne ƙasashen 3 suka tattaunawa domin shimfiɗa wannan bututu mai tsawo kilomita dubu 4 da 128, kuma tun a wancan lokaci an kiyasta cewa ana bukatar Dala bilyan 10 domin aiwatar da aikin.

Rikicin Rasha da Ukraine ne ya ƙara zaburar da waɗannan ƙasashe domin gaggauta aiwatar da wannan aiki na bututun iskar gas, musamman lura da cewa tun a 2022 mafi yawan ƙasashen Turai sun bayyana aniyarsu ta daina dogara da Rasha domin samun makamashin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp