Kungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta nemi kamfanonin sadarwar da ke aiki a kasar su janye sabon farashin su kuma koma wa tsohon farashi cikin gaggawa.
A wata takardar bayan taro da ƙungiyar ta fitar wanda ta gudanar ranar Talatar nan a birnin Lokoja na jihar Kogi, NLC ta ɗauki wasu matakai guda bakwai kan al’amarin kamar haka:
- Janye ƙarin farashin da komawa tsohon farashi har zuwa lokacin da kwamitin da ƙungiyar ta kafa ya kammala gudanar da bincike.
- Ƙungiyar ta buƙaci ma’aikatan Najeriya da sauran ƴan ƙasa da su ƙaurace wa kiran waya ko amfani da datar kamfanonin MTN da Airtel da Glo a kowacce rana daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa ƙarfe 2:00 na rana na kowace rana har zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
- Ta umarci ƴan Najeriya da su daina sayen data daga kamfanonin
- Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Najeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ƴan ƙasar
- Ƙungiyar za ta jagoranci rufe ayyukan kamfanonin ranar 1 ga watan Maris idan dai har ba su janye sabon ƙarin da suka yi ba ya zuwa ƙarshen watan Fabrairu.
- Ƙungiyar ta umarci dukkannin rassanta na jihohi da su zaburar da mambobinsu gabanin 1 ga watan na Maris.
- Ƙungiyar ta umarci dukkan sauran sassanta da su ja hankalin mambobinsu wajen ƙaurace wa kira ko amfani da datar kamfanoni a sa’o’in da aka ayyana
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1487 days 17 hours 27 minutes 51 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1469 days 19 hours 9 minutes 16 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com