An gudanar da Jana’idar Dan Zago

An gudanar da jana’izar Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Dan Zago, tsohon shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano.

An gudanar da jana’izar a Kofar Kudu, dake fadar mai martaba Sarkin Kano Dr. Muhammadu Sanusi II.

Jana’izar ta samu halartar fitattun mutane da suka hadar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Dan Zago, ya rasu yana da shekaru 74, sannan ya bar Mata 4 da yaya 37 sai kuma jikoki da dama.

Bayan kammala jana’izar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya jagoranci zuwa gidan marigayin, domin yi musu ta’aziyyar rashin da suka yi.

Sauran wadanda suka je ta’aziyyar sun hadar da tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo da shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Ismail Jibrin Falgore sun shiga gidan marigayin inda suka yi addu’oi domin nema masa gafarar Allah.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1486 days 9 hours 52 minutes 15 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1468 days 11 hours 33 minutes 40 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com