Home General Majalisa na son shugaban kwastam ya yi bayani kan ƙin yi wa...

Majalisa na son shugaban kwastam ya yi bayani kan ƙin yi wa wasu manyan jami’an hukumar ritaya

Kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya kan karɓar ƙorafe-ƙorafen jama’a ya gayyaci babban kwanturolun hukumar kwastom na ƙasar, Adewale Adeniyi domin ya yi mata bayani kan abin da ya sa wasu manyan jami’an hukumar suka ƙi yin ritaya duk kuwa da lokacinsu ya yi.

Cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai na kwamitin, Chooks Oko ya fitar, ya ce an gayyaci babban jami’in hukumar ne domin ya yi bayani kan ƙorafin da aka shigar wa kwamitin dangane da ƙin yin ritaya da wasu manyan jami’an hukumar suka yi bayan lokacinsu na hakan ya yi.

Gidauniyar Obasi-Pherson Help ce ta shigar da ƙorafin gaban kwamitin, inda ta yi zargin cewa wasu jami’an hukumar masu muƙamin mataimakin kwanturola da masu muƙamin kwanturola sun ƙi ajiye aikinsu, bayan cikar lokacin.

Yayin bayar da sammacin, majalisar wakilan ta ce babban kwnturolan ƙasar ne kaɗai ke da haƙƙi bayyana wa ‘yan ƙasa ainihin gaskiyar wannan zargi.

“Ƴan Najeriya sun cancanci sanin gaskiyar abin da ya faru daga bakin babban konturolan…, a wannan lokaci da mafi yawan matasanmu ke neman ayyukan yi, indai batun nan gaskiya ne, to babu adalci ace ga wasu tsofaffin da suka isa ritaya su ƙi yin hakan,” a cewar shugaban kwamitin, Mike Etaba.

Ya ƙara da cewa ”ba wai muna ɗaukar ɓangare ba ne, muna nazarin kowane batu ne bisa gaskiya domin tabbatar da adalci ga waɗanda suka cancance shi”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp