Home General MTN ya nemi gafarar ƴan Najeriya kan ƙarin kuɗin kira da na...

MTN ya nemi gafarar ƴan Najeriya kan ƙarin kuɗin kira da na data

Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya bai wa masu amfani da layukansa haƙauri kan ƙarin kuɗin kira da na data da kamfanin ya yi a ƴan kwanakin nan.

A farkon makon nan ne aka wayi gari da ƙarin kusan kashi 200 cikin ɗari, lamarin da ƴan ƙasar da dama suka yi Allah wadai da shi.

To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a shafinsa na X, ya ce yana sane da yadda masu amfani da layukansa suka nuna damuwa bayan da suka wayi gari kwatsam da ƙarin kusan kashi 200 na kuɗin data.

Kamfanin ya ce zai iya bayar da dalilan da suka sa ya ɗauki matakin ƙarin, to sai dai ya ce in ma ya yi hakan ba zai gamsar ba.

”Saboda da haka mun karɓi laifinmu, mun yi kuskure, muna bayar da haƙuri kan hakan, a kuma yafe mana”, a cewar kamfanin.

Ƙarin dai ya tayar da ƙura a Najeriya, lamarin da ya sa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar, NLC ta buƙaci al’umma su ƙaurace wa amfani da layukan manyan kamfanonin wayar daga ƙarfe 11 na safe zuwa 2:00 na rana a kullum daga yau Alhamis, 13 ga watan Fabarairu har zuwa 28 ga watan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp