Home General Ma’aikatan ofisoshin jakadancin Najeriya na kokawa kan rashin biyan su albashin watanni

Ma’aikatan ofisoshin jakadancin Najeriya na kokawa kan rashin biyan su albashin watanni

Aƙalla ma’aikata 450 ne da ke aiki a ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashe 109 ba su samu albashinsu ba na wata biyar zuwa shida.

Ma’aikatan da ke ƙarƙashin ma’aikatar harkokin wajen kasar na cikin mawuyacin hali na rashin kuɗi ta yadda wasunsu ba ko iya biyan kuɗin haya da kuɗin makarantar ‘ya’yansu ko biyan wasu muhimman buƙatun iyalinsu kamar yadda Jaridar PUNCH ta ruwaito.

Mai riƙon muƙamin kakakin ma’aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce ma’aikatar na sane da wannan hali da ma’aikatan ke ciki, ya kuma bayar da tabbacin cewa za a shawo kan matsalar.

Manyan jami’an fadar gwamnatin tarayya da kuma jami’an da ke aiki a ma’aikatar harkokin wajen Najeriya sun bayyana wa jaridar cewa ana buƙatar dala biliyan ɗaya domin biyan bashi da kuma tafiyar da harkokin ofisoshin jakadancin ƙasar daban-daban a ƙasashen duniya.

A lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki ya sake nazarin manufofin waje na ƙasar inda ya dawo da jakadu 83 a watan Satumba na 2023.

Sai dai kuma matsalar rashin kuɗi ta haifar da jinkiri wajen naɗa sababbin jakadun har yanzu.

To amma jaridar ta ruwaito cewa rashjin naɗa jakadun ya ƙara haifar da jinkiri wajen biyan albashin ma’iakatan ofisoshin jakadancin na Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp