Gwamnatin Najeriya ta umarci ‘Yan Sandan ƙasar da su daina holin masu laifin da suka kama.
Ministan shari’a, Latif Fagbemi, ne ya bawa rundunar ‘yansandan umarnin, na ta daina holin wadanda ake zargi da laifi bayan ta kama su.
Read Also:
Wasu manyan jami’an rundunar a Abuja da Lagos sun tabbatar wa da jaridar Punch cewa, tuni umarnin da suka karɓa ya fara aiki tun ranar Lahadi da ta gabata.
A baya dai rundunar ‘yansandan tana yin holin waɗanda ta kama ɗin ne, ga ‘yan jaridu ko kuma ta shafukan ta na sada zumunta tun kafin ta gurfanar da su a gaban Kotu.