Home General Gwamnoni 20 a Najeriya sun ƙi biyan mafi ƙarancin albashin dubu 70,000

Gwamnoni 20 a Najeriya sun ƙi biyan mafi ƙarancin albashin dubu 70,000

Shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi ta Najeriya ALGON Alhaji Haruna Ƙanƙara, yace har yanzu akwai jihohi 20 a ƙasar da basu fara biyan sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 ga ma’aiktan ƙananan hukumomi da malaman makarantun firamare ba.

Shugaban ya ce jihohin sun haɗa da Yobe da Gombe da Zamfara da Kaduna da Imo da Ebonyi da Cross River da Abuja fadar gwamnatin ƙasar da Borno da sauransu.

Shugaban na NULGE ya yi wannan bayani ne a yayin wata zantawa da ya yi da jaridar Punch ta Najeriya, tare da ba da hankali akan biyan mafi ƙarancin albashin a ɓangaren ma’aikatan ƙananan hukumomi da Malaman Makarantun firamare.

Shugaban na Najeriya ya rattaɓa hanu kan ƙudirin dokar biyan naira dubu 70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan ƙasar ne a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 2024, bayan wata yarjejeniya da suka cimma da jagororin ƙungiyar kwadago ta ƙasar.

An kara sabon mafi karancin albashin ne da kashi 133 wato daga N30,000 zuwa N70,000, a daidai lokacin da kasar ke fama da tabarbarewar tattalin arziki.

Da yake bayani kan yadda ake aiwatar da dokar, Kankara ya ce, “A gaskiya muna fuskantar kalubale a jihohi da dama, kamar kimanin 20 da har yanzu basu fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi ba.

Ƙanƙara ya ci gaba da cewa ”akwai jihohi kamar Sokoto da Yobe da Gombe da da Zamfara da Kaduna da Imo da Ebonyi da Borno da Cross River da Abuja fadar gwamnatin ƙasar da sauran su, a yayin da wasunsu sun fara biyan sabon tsarin a mataki na jiha sai kuma suka yi watsi da na ƙananan hukumomi da Malaman makarantu, amma muna cigaba da fafutukar ganin an yiwa ma’aikatan adalci”.

Shugaban ya ƙara da cewa “wani ɓangare kuma wasu daga cikin gwamnonin sun alƙawarta cewa zasu biya amma suka gagara biya, sai dai muna iya ƙoƙarin ganin an shawo kan wannan matsalar”

Sannan dangane da batun aiwatar da ‘yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi kuwa, shugaban NULGE ya bayyana cewa har yanzu babban bankin kasar bai tattauna da majalisun ba kan bude asusun ajiyar banki.

“Abin da kungiyar ta ke bukata a koda-yaushe shi ne babban bankin Najeriya ya fitar da wani tsari ga kananan hukumomi da zai basu damar bude asusun ajiya da su, amma har yanzu ba a samu hakan ba”.

Sai dai Shugaban NULGE na jihar Kwara, Seun Oyinlade, ya ce gwamnatin jihar sa ta fara biyan Naira 70,000 ga ma’aikatan jihar tun a watan Oktoban shekarar 2024.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp