Bincike: Shin da gaske ne Babban Bankin Nijeriya ya samar da takardar kudi ta naira dubu N5,000 da dubu N10,000 da zata fara yawo a gari daga 1 ga watan Maris?

‎Ikirari: Wani rubutu da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani da suka hadar da Facebook da shafin X da aka sani da Twitter, ya bayyana cewa babbana bankin Nijeriya (CBN) na shirin samar da takarda kudi ta naira dubu 5 da dubu 10 dake dauke da hotunan manyan shuwagabannin Nijeriya. Dalilin yin takardun kudin kuma shine domin samar da mafita ga matsalar ƙarincin takardun ƙudi da ake fada da shi a ƙasar. Wallafar dai da bayyana cewa ana tsammanin kuɗin za su fara fitowa cikin al’umma daga 1 ga watan  Mayun 2025. Wanda a jikin rubutun aka hada da hotunan sabbin takardun ƙudin.

Labarin da aka wallafa a ranar 2 ga watan Afrilun 2025, aka kuma alaƙantashi da babban bankin ƙasar cewa ya gabatar da sabbin kudin a hukumance da suka haɗar da Naira dubu 5 da dubu 10 a matsayin wani yunƙuri na daidaita hada-hadar kudi da kuma haɓaka tsarin.

A cikin sanarwa, mai dauke da sa hannun mataimakin Gwamnan babban bankin, Dr. Ibrahim Tahir Jr., ta ce samar da sabbin kuɗin zai taimakawa ƴan Nijeriya matuƙa wajen gudanar da harkokin kuɗi masu tarin yawa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. haka kuma sanarwa ta kara da cewa matakin ya yi daidai da yadda tsarin ke tafi a duniya gami da inganta harkokin tattalin arziki.

Labarin ya ce naira dubu N5 din na dauke da hoton Chief Obafemi Owolowo, ya yi da naira dubu N10 ta ke dauke da hoton Dr. Nnamdi Azikiwe, wanda haka ke matsayin wata girmamawa a garesu bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban ƴan Nijeriya. Haka kuma kuɗin na kunshe da ingantaccen tsaron kudi da suka hadar da launi da dai sauransu.

Sanarwar da bayyana cewa kuɗin zasu isa hannun mutane daga ranar 1 ga watan Mayun 2025, ta kuma umarci bankunan kasar da su tabbatar da sun sanya ta a na’urar cirar kudi ta ATM da kuma cikin bankunan ga wadanda za su karɓi kudin a hannu. Haka kuma sanarwa ta shawarci al’ummar ƙasar da su tabbatar da sun kai an sauya musu tsuffin kudaden su daga 30 da watan Yunin 2025.

An saka adireshin  cbn.gov.ng/newcurrency, da samfurin kudin a cikin sakon da aka wallafa.

Tarihin yadda Babban Bankin Nijeriya ke gabatar da sabbin kuɗi:

‎Babban bankin Nijeriya (CBN) shi yake da alhakin samarwa da kuma lura da kudin al’ummar Nijeriya. Ta karkashin sashen dake lura da gudanarwar kudi na babban bakin ƙasar da aka fi sani da (Currency Operations Department) shi ke da alhakin samarwa, lura, rabawa da kuma ƙone wadanda suka lalace cikin takardun kudin da tsaba.

Tun bayan gabatar da kudin ƙasar a shekarar 1973, an sami ƙarin samfurin kudin da suka hadar da N 50 a shekarar 1991, N 100 a shekarar 1999, N 200 a shekarar 2000, N 500 a shekarar 2001 da kuma N 1,000 a shekarar 2005. Naira dubu daya ta sami sauye sauye  na inganta tsaron kuɗi da suka hadar da sauya launi da kuma kirar kuɗin.

A shekarar 2007, an samar da kudin samfurin leda wato (Polymer) na ₦5 zuwa ₦50, ledar kuɗi ta ₦20 ita ce ta farko a cikin kudin leda a shekarar 2009, daga bisani aka samar da ₦5, ₦10, and ₦50. Haka kuma an ƙaddamar ₦100 ta musamman a shekarar 2014 ga al’ummar Nijeriya, wadda aka mata salo na musamman domin tarihi.

A shekarar 2022, babban bankin na CBN ya bayyana yunƙurinsa na sake fasalin kudin domin tallafawa tsarinsa na komawa amfani da hanyar hada-hadar kudi ta zamani (digital currency). Wannan yunkuri na sabunta kudin an kaddamar da shi ne a watan Disambar 2022, ta inda dukkan kudin dake yawo a hannun mutane zai koma banki a karshen shekarar 2023. Sai dai yunkurin ya haifar da matsala a bangaren hada-hadar kudin wanda ya kai ga haifar da zanga-zanga a kasar.

Duk da wannan ƙalubale da aka samu, bankin CBN ya mayar da hankali gami da jajircewa da kare mutuncin naira ta hanyar sabuntawa lokaci zuwa lokaci da samar da tsaron nairar.

Tabbatar da Sahihancin labari: Domin tabbatar da sahihani ikirarin da ke yawo a kafafen sada zumunta ta zamani, tawagar masu bincike sahihancin labari ta PRNigeria sun yi amfanin da na’ura binciken hoto ta Reverse Image Search kan ikirarin da aka wallafa a shafin X da aka fi sani da twitter a watan afrilun 2025.

‎‎bayan binciken da tawagar suka kara faɗaɗawa kan wannan sanarwa da ta ambaci “Dr. Ibrahim Tahir Jr”. matsayin mataimakin Gwamnan babban bankin dake lura da sashen kuɗi da gudanarwa na bankin. Binciken ya duba shafin bankin da kuma rahoton shugabancin bankin ya nuna babu wani mai irin wannan sunan da ya gama aiki ko kuma yake aiki a halin yanzu. Babban bankin Nijeriya yana da maitaimaka Gwamnan guda hudu, waɗanda sunayen su yake a bayyana ne amma babu sunan Ibrahim Tahir Jr.

Bugu da ƙari, hotunan dake yawo a kafafen sada zumuntar na ₦5,000 da ₦10,000 musamman manhajar WhatsApp, Facebook da Instagram basu da ingantaccen tsarin zane.

Wani bincike na kai da kai da PRNigeria ta gudanar ya bayyana wasu kura –kura da suka bayyana akan iƙirarin sabbin takardun kudin da suka hadar da:

Rashin daidaituwar rubutun jikin kudin  idan aka kwatanta da wadanda ake amfani da su tun da fari (takardun kudin Nijeriya)

Rashin bayyanar alamun tsaron takardun kudi da suka hadar da:

Wani buyayyen zane (Watermarks)

Tsaron jikin kudi

Launin samfurin kudi

Launin takardun kudin

Wasu daga cikin hoton dake jikin takardun da ake zargin sune sabbin ƙudin, sun nuna an kwafo su ne a jikin tsuffin kuɗin kasar ko kuma kudin ƙasashen waje.

Launin da aka yi amfani da shi a jikin kuɗin ya nuna cewa an yi amfani da na tsuffin kuɗin ne karara.
Hakazalika, babban bankin na Nijeriya yana gudanar da ayyukan sadarwarsa ta tsatstsauran yanayi. Dukkannin wani mataki mai muhimmanci, musamman wanda ya shafi harkokin kudi, yakan yada ta kafafensa na da suka hadar da:

CBN’s official website

Shaharrun shafukansa na sada zumunta (misali., @cenbank on X/Twitter)

Taron ganawa da manema labarai da kuma takardar sanarwa.

Jaridun kasa da kuma jaridu masu zaman kansu.

A lokacin da mu ke gudanar da wannan bincike babu wata sanarwa daga wadancan shafuka da ta fito.

Amma, bankin na CBN ya musanta jita-jita, in da ya fitar da sanarwar kai tsaye cewa al’umma su yi watsi da dukkanin nau’in labarai na karya da ake yadawa. A cewa CBN:

Wannan labarin ba daga Babban bankin Nijeriya yake ba. Ku fahimci cewa shafin internet mallakin CBN shine cbn.gov.ng.”

‎Kammalawa: binciken sahihancin labarai da PRNigeria ta gudanar kan iƙirarin da ke cewa babban bankin Nijeriya ya gabatar dabbin takardun kudi na ₦5,000 da ₦10,000, ta gano labari ne ba na gaskiya ba. Sanarwar da ke yawo kamar wutar daji a cikin al’umma ba daga CBN ta fito ba, haka kuma bankin ya ce bashi da wata alaka da ita.

Hukunci: PRNigeria ta tabbatar da cewa wannan iƙirarin ƘARYA ne!

PRNigeria

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1462 days 14 hours 58 minutes 10 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1444 days 16 hours 39 minutes 35 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com