Home General Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa...

Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafi

Gwamnatin Jihar Kano ta fara aikin tantancewa tare da ɗaukar bayanan ’yan kasuwar da gobarar kasuwar Singer ta shafa domin tsara yadda za a bi matakan ba su tallafi.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da yammacin ranar Asabar inda ta ƙone shaguna da tebura fiye da 1,500, lamarin da ya jawo asarar dukiya mai yawa ga ’yan kasuwa.

Tuni gwamnatin tarayya ta bai wa waɗanda abin ya shafa tallafin Naira biliyan biyar, baya ga gudummawar da wasu hukumomi da daidaikun jama’a suka bayar.

Hukumomin jihar sun sanar da fara aikin tantance ’yan kasuwar ta hannun Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha wato SEMA.

Hukumar ta bayyana cewa duk lokacin da aka samu iftila’i irin wannan, sukan je su ƙididdige tare da ɗaukar bayanan waɗanda abin ya shafa domin sanin yadda za a taimaka musu.

Shugaban hukumar, Isyaku Abdullahi Kubarachi, ya ce suna gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA reshen jihar Kano.

SEMA ta ce aikin zai ɗauki kwanaki biyar ana yi, bayan haka za su rubuta rahoto su miƙa wa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, wanda ake sa ran zai yi nazari tare da kafa kwamitin da zai kula da raba tallafin ga waɗanda suka cancanta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp