Jakadan Amurka a yankin Afirka Mike Hammer, ya gana da mataimakin firaministan kasar Habasha Demeke Mekonnen a birnin Addis Ababa a ranar Juma’a, a kokarinsa na kawo karshen rikici a arewacin kasar.
Bayan wata ziyara da ya kai a watan Satumba na shekarar nan, Mike Hammer ya koma yankin tun ranar 3 ga watan Oktoba, da fatan ganin an dakatar da tashin hankali a arewacin Habasha nan take da kuma goyon bayan kaddamar da tattaunawar zaman lafiya a karkashin kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka.
Read Also:
A farkon watan Oktoba ne gwamnatin tarayya ta Firaminista Abiy Ahmed da wakilan ‘yan tawaye a yankin Tigray suka ce a shirye suke su je tattaunawar da kungiyar kasashen afirka ta AU ta gayyace su a Afirka ta Kudu.
Sai dai ba a iya gudanar da wannan tattaunawa ba, musamman saboda matsalolin kungiyoyi da na kayan aiki, a cewar jami’an diflomasiyya.
A ranar Juma’a, yayin tattaunawa da Hammer, firaministan kasar Habasha Demeke wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, ya jaddada aniyar gwamnati na ganin an warware rikicin arewacin kasar cikin lumana”, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta wallafa a shafinta na twitter.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 16 hours 16 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 58 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com