Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce janar-janar da ke rikici a Sudan sun amince sun tsagaita wuta ta kwana uku ranar Litinin, bayan an kwashe kwana 10 ana fafatawa tsakaninsu.
Yarjejeniyoyin tsagaita wutar da suka kulla a baya ba su yi tasiri ba lamarin da ya kai ga kisan daruruwan mutane da kuma raba dubbai daga gidajensu.
Sai dai Blinken ya ce “bayan an kwashe sama da awa 48 ana tattaunawa sosai, Rundunar Sojin Sudan da Rapid Support Forces (RSF) sun amince su aiwatar da jarjejeniyar tsagaita wuta ta awa 72 daga ranar Litinin da daddare.”
Sakataren Wajen Amurka ya yi kalaman ne awa biyu kafin a soma aiwatar da yarjejeniyar.
Hakan na faruwa ne a lokacin da Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa Sudan na “dab da fadawa cikin bala’i” sakamakon rikici tsakanin bangarorin biyu, wadanda ke fafatawa a Khartoum da wasu bangarori na kasar.
An kashe akalla mutum 427 yayin da fiye da mutum 3,700 suka jikkata sakamakon rikicin, a cewar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.
Wani babban jami’in ofishin jakadancin Masar a Khartoum yana cikin wadanda aka kashe a baya bayan nan, a cewar ma’aikatar wajen kasar.
An kashe shi ne yayin da yake kan hanyar zuwa ofishin jakadancin domin sanin halin da ake ciki game da yiwuwar kwashe su daga Sudan.
Rikicin na faruwa ne tsakanin runsunar sojin da ke karkashin Janar Abdel Fattah al Burhan da dakarun RSF da ke karkashin tsohon mataimakinsa Janar Mohamed Hamdan Dagalo.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 41 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 23 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com