Shugaban kamfanin sadarwa na Daar Communications Raymond Dokpesi, ya rasu ranar Litinin.
Rahotanni a Najeriya sun ambato iyalan mutumin mai shekara 71 na ba da sanarwar rasuwar tasa, amma ba su bayyana abin da ya yi ajalinsa ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gidan talabijin na AIT na ƙarƙashin kamfanin Daar Communications, wanda kuma ya mallaki gidan rediyon Ray Power.
“Cikin alhini da bakin ciki, muna sanar da rasuwar Chief Raymond Aleogho Anthony Dokpesi, wanda ya mutu ranar Litinin, 29 ga watan Mayu,” a cewar sanarwar.
Baya ga harkokin sadarwa, Dokpesi ɗan siyasa ne wanda ya taɓa neman takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP.
PRNigeria hausa












