Kashi biyu cikin uku na gidajen Najeriya ba su samun lafiyayyen abinci – NBS

Wani bincike da Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta gudanar ya gano cewa rashin wadata ya sa kashi biyu cikin uku na gidaje a Najeriya ba su iya samun lafiyayyen abinci mai ɗauke da ingantattun sinadarai.

Binciken da hukumar ta gudanar ya mayar da hankali ne kan ƙaruwar talauci a tsakanin gidajen ƙasar da irin tasirin da hakan ke yi wajen raguwar sayen abubuwa da ‘yan ƙasar suka yi sakamakon tashin farashinsu.

“Kusan kashi biyu cikin uku na gidajen Najeriya ba su iya cin lafiyayyen abinci mai ɗauke da sinadarai ko su dafa abinci saboda rashin wadata da suke fama da shi”, kamar yadda rahoton binciken ya nuna.

Haka kuma binciken ya gano cewa kashi 63.8 cikin 100 na gidajen ƙasar na cin abincin ɗan kaɗan saboda rashin kuɗi, yayin da kashi 62.4 na gidajen ke cikin fargabar rashin samun wadataccen abinci, sannan kuma kashi 60.5 cikin 100 na gidajen ba sa iya cin abincin da ya kamata a ce suna ci.

Rahoton binciken na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan da wani rahoto da gwamnatin Najeriya ta fitar tare da tallafin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa ‘yan ƙasar fiye da miliyan 33 za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a 2025.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 14 hours 53 minutes 8 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 34 minutes 33 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com