Home Labarai Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, kuma jigo a jam’iyyar haɗaka ta ADC ya nuna damuwa kan ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a da aka samu a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja na ranar Asabar, yana mai zargin cewa hakan na nuna yadda ake yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa yawan jama’ar da suka fito zaɓen Abuja bai kai kashi 20 cikin 100 ba wata alama da ke nuna halin da dimokuraɗiyyar Najeriya ke ciki a yanzu.

Ya ce “Ƙarancin masu kaɗa kuri’a da aka samu a babban birnin ƙasar ba abin mamaki ba ne, illa sakamakon yanayin siyasa da ya ce ya cika da rashin haƙuri da tsoratarwa da kuma rage ƙarfin muryoyin adawa.”

A cewarsa, “idan ’yan ƙasa suka daina yarda cewa ƙuri’unsu na da tasiri, dimokuraɗiyya ya fara mutuwa.”

Ya ƙara da cewa “abin da ake gani ba sakamakon rashin sha’awar zaɓe kaɗai ba ne, illa sakamakon shugabanci da ke takura tsarin dimokuraɗiyya.”

Ya ce “dimokuraɗiyya ba za ta cika ba idan babu ƙarfi a ɓangaren adawa, babu gasa ta gaskiya a siyasa, kuma babu amincewar jama’a.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Fasinjoji 18 Sun Mutu a Hatsarin Mota Yayin Dawowa Daga LegasGwamnatin Najeriya ta ƙudiri Anyiar Tara N2.5trn Daga Kuɗaɗen Shiga a 2026Wanda ya Kafa PRNigeria ya Nufi Kotu Don Daukaka Kara Kan Watsi da Karar ₦1bn da ya Shigar Kan NIPSSObi ya yi Tsokaci Game da Hukuncin da Kotu ta yi na Soke Rijistar Jam'iyyar NDC Soke Rijistar NDC Murƙushe Dimokuraɗiyya ne - PDPAn Gurfanar da ƙarin Mutane 17 kan Kashe Matar Aure a Jihar KadunaCutar Tamowa: Gwamnatin Kebbi ta Karyata Rahoton MSF Kan Mutuwar ƙananan  Yara a JiharJam'iyyar NDC ta Magantu Bayan Kotu ta Soke Rijistar taAbinda Ke Haddasa Matsalolin Tsaro a Jihar mu - Gwamnan Ahmed Aliyu Babban Bankin Najeriya ya Umarci Bankuna da su Rufe Asusun Mutane da Ake Zargin da Tallafawa Ta'addaci Sunayen Mutane 6 da Kamfanonin Canji 3 da Ake Zargin da Tallafa wa Ta'addaci a Najeriya Mun Ceto Mutane 47 Daga Hannun Mayaƙan ISWAP - Rundunar Sojin NajeriyaSanatocin za su Fara Duba ƙudirin  Kafa ƴan Sandan Jihohi Ranar Laraba - AkpabioMatakin da Amurka ta ɗauka na Cire Tallafin Cutar HIV a Afirka ta Kudu Zai Janyo Asarar Rayuka - MDDAn Gurfanar da Mutane 24 Bisa Zargin Kashe Matar Aure a Maraban Jos
X whatsapp