Mutane 2 Sun Rasa Rayukansu a Zaben Deleget na PDP a Jahar Osun
Akalla mutum biyu sun rasa rayukansu yayinda da dama suka jikkata a zaben deleget na jam’iyyar People’s Democratic Party PDP dake gudana a jihar Osun.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Yemisi Opalola, ta tabbatar da hakan ga manema labarai ranar Laraba a Osogbo, TVCNews ta ra
Read Also:
waito. A cewarta, an kashe wani matashi mai suna Toheeb Mutallib a Oke Oba, Agberire a karamar hukumar Iwo, yayinda aka kashe wani dan jam’iyyar siyasa Aremu Olamide a Ipetumodu, karamar hukumar Ife-North.
asu masu idanuwan shaida sun bayyana cewa an yiwa mutane da dama jina-jina yayinda yan daba suka kai hari garuruwa irinsu Ede, Osogbo, Odo-Otin, Olorunda, Iwo, da sauransu.
Hakazalika an bankawa mota wuta a Ipetumodu sakamakon rikici tsakanin yan daba.
Kawo yanzu Alkalin zaben, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmad Fintiri, basu isa wajen tattara zabe ba.
Za’a zabi mutum uku-uku a gundumomin jihar 332 kuma su zasu kada kuri’a a zaben fidda gwanin dan takaran gwamna a ranar 7 ga Maris, 2022.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1485 days 20 hours 31 minutes 54 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1467 days 22 hours 13 minutes 19 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com