Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta Saka Baki Cikin Rikicin Kasar Rasha da Ukraine
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta saka baki cikin rikicin da ke faruwa tsakanin kasar Rasha da Ukraine tana mai kira ga Rasha ta mayar da dakarunta gida.
Najeriya ta yi wannan kiran ne a wani taro da ta yi da wakilan kasashen G7 a ranar Juma’a a Abuja inda ta yi kira da bangarorin biyu su rungumi diflomasiyya da zaman lafiya.
Jakadan Jamus kuma shugaban G7, Birgitt Ory, ya yi wa Najeriya godiya bisa tofa saka baki a lamarin tana mai cewa muryar Najeriya na da muhimmanci a duniya kuma ya dace a ji matsayarta
Abuja- Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gana da wakilan kasashen G7 a Najeriya inda ta nuna damuwar ta game da rikicin Rasha da Ukraine tana mai kira da a warware lamarin cikin zaman lafiya, rahoto Daily Trust.
Ministan harkokin kasashen waje, Goeffrey Onyeama, ya gana da wakilan a ranar Juma’a a Abuja, yana mai cewa gwamatin Najeriya ta yi kira da a zauna lafiya kuma a yi amfani da diflomasiyya da wurin warware matsalar cikin lumana.
Read Also:
Onyeama ya ce Najeriya bata goyon bayan matakin da Rasha ta dauka na amfani da karfin soji, tana mai kira ga Rasha ta janye dakarunta, rahoton The Punch.
“Dukkan bangarorin biyu su mayar da hankali wurin zaman lafiya da diflomasiyya.
“Muna goyon bayan duk wani mataki na dakatar da harin soji kuma dakarun Rasha su janye su koma Rasha,” a cewar Onyeama.
Jakadan Jamus ya yaba da matsayar Najeriya kan rikicin na Rasha da Ukraine
Da ya ke magana da manema labarai bayan taron na sirri, Jakadan Jamus a Najeriya, Birgitt Ory, wanda kuma shine shugaban G7 ya yaba da matakin Kungiyar Hadin kan Afirka, AU, kan rikicin.
Ory, wanda kuma ya jinjinawa Najeriya kan tofa albarkacin bakinta, ya ce Najeriya muhimmiyar murya ce da ya dace duniya ta ji daga gare ta.
Ya ce abin da ke a fili shine tir da hare-haren da dukkanin kasashen Majalisar Dinkin Duniya suka yi sakamakon harin da Rasha ta kai.
Ory ya ce matakan da Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Kare Hakokin Bil Adama, wacce Najeriya mamba ce da wasunsu suka dauka yana da muhimmanci.
Sauran wadanda suka hallarci taron sun hada da jakadun Amurka, Birtaniya, EU, ECOWAS, Japan da Canada.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 19 minutes 16 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 41 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com