Kotu ta Kwace Kujerar Gwamnan Jahar Ebonyi da Mataimakinsa Kelechi Igwe

Kotu ta Kwace Kujerar Gwamnan Jahar Ebonyi da Mataimakinsa Kelechi Igwe

Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da mataimakinsa Kelechi Igwe sun rasa kujerunsu saboda ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Kotun ta yanke hukuncin cewa kuri’un da suka samu yayin zaben gwamna na jam’iyyar PDP ne don haka Umahi da mataimakinsa sun rasa kuri’un bayan ficewarsu daga jam’iyyar.

Kotun ta umurci INEC ta karbi zabin sunayen wadanda za su maye gurbin Umahi da mataimakinsa daga PDP ko kuma ta sake sabon zaben gwamna a jihar.

FCT, Abuja – Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Talata, a kori Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da Mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe, bayan sun fice daga jam’iyyar PDP sun koma APC mai mulkin sa, rahoton Vanguard.

Kotun, a hukuncin da Mai sharia Inyang Ekwo, ya yi, ta ce kuri’u 393,042 da Gwamna Umahi ya samu a zaben ranar 6 ga watan Mari na gwamnan Jihar Ebonyi, na jam’iyyar PDP ne kuma doka bata amince a mayarwa APC ba.

A cewar kotun, bayan komawa jam’iyyar APC, Umahi da mataimakinsa, ba PDP kadai suka bari ba, sun raba kansu da kuri’u jam’iyyar ta PDP, Daily Trust ta rahoto.

Kotun ta ce idan aka yi la’akari da sakamakon zaben na gwamna, kujerar gwamnan Jihar Ebonyi da mataimakinsa, ‘mallakar wanda suka yi karar ne ba wata jam’iyyar daban ba.’

“Babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin kasa da ya nuna ana iya musayar kuri’u daga jam’iyya daya zuwa wata jam’iyyar.”

Ta ce jam’iyyar PDP ce ke da kuri’un da kujerun da masu zabe a Jihar Ebonyi suka kada, don haka ba za a iya mika wa Gwamna Umahi da mataimkinsa kuri’un ba idan sun fice daga jam’iyyar.

Don haka kotun ta bada umurnin cewa nan take Dave Umahi da Igwe su ajiye mukamansu.

Kotu ta umurci INEC ta karbi sunayen wadanda za su maye Umahi da mataimakinsa daga PDP ko ta sake sabon zabe

Ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta karbi sunayen mutanen za su maye gurbin Umahi da mataimakinsa daga PDP, ko kuma ta sake yin sabon zabe a jihar Ebonyi kamar yadda sashi na 177(c) na kundin tsarin mulki da aka yi wa kwaskwarima ya ce.

Kotun ta kuma hana Umahi da mataimakinsa Igwe cigaba da amsa sunan gwamna da mataimakinsa na jihar Ebonyi.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan karar da jam’iyyar PDP ta shigar bayan Umahi da mataimakinsa sun koma APC.

Saurari karin bayani …

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 15 hours 17 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 41 minutes 42 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here