Har Yanzu ba mu Samu Sahihin Kwafin Takardar Hukuncin Kotu na Tsige Gwamnan Ebonyi ba – INEC
Hukumar zabe INEC tace har yanzun ba ta samu sahihin kwafin takardar hukuncin Kotu na tsige gwamna Umahi ba.
Kwamishinan INEC na kasa ya ce da zaran sun samu takardar daga Kotu, za su kira zama domin nazari kanta.
Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja ta kwace kujerar gwamna da kuma mataimakinsa na jihar Ebonyi kan sauya sheka.
Abuja – Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC tace har yanzun ba ta samu kwafin takardar hukuncin da babbar Kotun tarayya dake Abuja ta yanke kan Gwamna Dave Umahi da mataimakinsa ba.
Festus Okoye, Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin tara bayanai, ne ya faɗi haka yayin zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Abuja.
Premium Times ta rahoto Mista Okoye na cewa INEC zata zauna kan lamarin da zaran ta karbi takardar hukuncin da Kotu ta yanke.
Kwamishinan INEC ɗin ya ce:
Read Also:
“Har yanzun ba’a aiko mana da kwafin hukuncin da ake cewa Kotu ta yanke ba. INEC zata zauna ta yi nazari da zaran an miƙa mata takardar hukuncin Kotu ta gaske.”
Ko wane hukunci Kotu ta yanke?
A ranar Talata, babbar kotun tarayya dake zaune a Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Ekwo, ta umarci gwamnan Ebonyi, David Umahi, ya fice da ofis ɗin gwamna kan sauya shekar da ya yi daga PDP zuwa APC.
A hukuncin da Alkalin Kotun ya yanke, ya kuma umarci Mista Igwe da ya daina nuna kansa a matsayin mataimakin gwamnan jihar Ebonyi.
Mai Shari’a Ekwo, ya bayyana cewa tun da sun fice daga PDP, jam’iyyar da mutane suka zabe su karkashinta, kama ta ya yi mutanen biyu su yi murabus daga kan mukamanssu.
Ya kuma ƙara da cewa saɓa wa doka ne ɗan takarar da aka zaɓe shi a wani muƙami karkashin jam’iyyar siyasa kuma ya koma wata jam’iyya ta daban.
Ya ce kuri’un da gwamna Umahi ya samu a zaben 9 ga watan Maris, 2019 na jam’iyyar PDP ne ba na APC ba.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 32 minutes 26 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 13 minutes 51 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com