Sayen form din takarar gwamna da injinya Magaji Mu’azu yayi yaja cece-kuce
Read Also:
Sayen form din takarar gwamna da injinya Magaji Mu’azu yayi yaja cece-kuce
Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano ya sayi fam din tsayawa takarar Gwamnan jihar karkashin Inuwar Babbar Jam’iyya adawa ta PDP.
Ya shaidawa Politics Digest cewa zai rika bayyanawa magoya bayan sa muhimman kudirce kudircen daya yake dasu, da kuma fannin da zai mayar da hankali kacokan a yayin da yake fafutukar daukar wannan muhimmin nauyin.
“Wannan tafiya nasara ce ga Al’umma Kano da kuma Arewacin Nijeriya da kasa baki daya.
“Zahiri mun dauki gabarar tafiyar Kano Sabuwa, bayan mun roki tai makon Allah, muna bukatar Addu’oin Al’umma da goyan bayan su” in ji Mu’azu.
Mu’azu Ahmad Magaji, wanda aka fi sani da (Dansarauniya) injiniyan Man Fetur da Iskar Gas dan fafutuka kuma guda cikin ‘yan siyasa a Nijeriya dan asalin Jihar Kano.
An haifeshi a kauyen sarauniya dake Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano.
ya sami shaidar kammala Makarantar Firamare a shekarar 1980; ya kuma halarci Makarantar Sakandire ta Dawakin Tofa a tsakanin 1980 zuwa 1980, ya yi karatun Diploma a fannin Injiniya a kwalejin kere-kere ta jihar Kano (Polytechnic) a shekarar 1989. Ya kuma sami Digrin sa na farko a wannin fanni na Injiniya a Jami’ar Bayero dake jihar Kano, inda ya sami Digrin Sa na biyu a jami’ar Robert Gordon a shekarar 2000. Ya kuma sami cancanta a fannin sarrafa ayyukan, Injiniyan Rijiyar Man Fetur da Iskar Gas, Kimiyyar kasa da Bayanai a shekara 2006.
Mu’azu ya fara aiki a Hukumar Da’ar Ma’aikata ta Jihar Kano a shekarar 1989 ku ya yi ritaya a shekarar 2009, in da ya fara aiki da kamfanin Mai na shell har na tsawon shekaru 10
A shekara 2010 Shugaban Kasa Godluck Jonathan ya nada shi matsayin ko’odinata na Shirin gwamnatin tarayya na Sure-P inda yayi aiki daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2013.
Ya kuma yi aiki tare da gwamnan Jihar Kano Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin Babban Mataimaki na Musamman Kan Tsare-Tsare tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015. Ya kuma tsaya takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kano a shekarar 2014 ya kuma janye kafin gudanar da zaben cikin gida (Primary Election).
An kuma nada Mu’azu matsayin Kwamishinan Ayyuka a karkashin Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a shekarar 2019, in da aka cire shi daga mukamin a shekarar 2020 lokacin da yayi wani kalamai da akayi zargin na rashin da’a ne game da mutuwa Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Abba Kyari, wanda ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Corona (COVID-19).
Daga bisani Mu’azu ya kamu da cutar ta corona bayan gwajin da aka gudanar a kan sa inda aka killace shi, daga bisani kuma aka sallame shi bayan an gudanar da gwajin daya nuna ya warke daga cutar ta corona.
Sai dai Gwamnan jihar kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sake nada shi a Mukamin Shugaban Kwamitin Sanya Idanu kan yadda Aikin Shimfida Bututun Iskar Gas na NNPC-AKK da kuma habaka Masana’antun Jihar Kano.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 14 hours 36 minutes 43 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 18 minutes 8 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com