Wasu Karin Kwamishinonin da Mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da suka hadar da Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Sunusi Sa’idu Kiru da babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar kano Faruq Sule Garo sun yi murabus daga mukaman su.
Ta cikin takardar Murabus da kwamishinan Ilimin Sunusi Sa’idu Kiru ya aiki wa gwamnan, ya gode masa matuka bisa damar da ya bashi na yiwa al’umma aiki a karkashin gwamnatin sa.
Read Also:
Ganduje ya bayar da umarni ga dukkan masu Muradin tsayawa Takara a cikin jami’an Gwamnatin Jihar Kano suyi murabus daga nan zuwa ranar litinin. Umarnin da yayi daidai da sashe na 84(12) na sabuwar dokar zabe da aka yiwa gyaran fuska.
Tuni dai wasu kwamishinoni uku daga cikin kwamishinonin kunshin gwamantin Jihar Kano suka sanar da ajje aikin nasu, ta cikin takaddun sanarwa da suka aike ga Gwamnan.
Kwamishinonin sun hadar da Kwamishinan Kananan Hukumomi Murtala Sule Garo, Kwamishinan Karkara Musa Iliyasu Kwankwaso da na Kasafi da Tsare Tsare Nura Dankadai.
Sunusi Kiru ya bayyana Murabus din nashi matsayin abinda zai bashi damar wakiltar Bebeji/Kiru a Zauren Majalisar Wakilan Nijeriya.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 8 hours 48 minutes 29 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 10 hours 29 minutes 54 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com