Rundunar Sojin Nijeriya tace ta dukufa wajen bankadowa tare da tseratar da kwamandan sojan da yayi batan dabo yayin gudanar da atisayen kawar da ‘yan ta’adda a jihar Taraba.
Wannan nakunshe ne ta cikin wata takarda mai dauke da sahannun Daraktan yada labaran Rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu.
Dakarun dai sun sami kiran waya dake tabbatar da cewa kauyen na Tati na fuskantar harin ‘yan bindiga, sai dai a kokarin sun a fatattakar ‘yan ta’addar suka fada komar su, inda sojoji 6 suka kwanta dama, yayin da babban jami’in soji guda ya bata.
Read Also:
Sai dai Rundunar hadin Gwuiwa ta dakarun sojin da suka kai dauki kauyen Ananum dake karamar hukumar Donga ta jihar, sun hallaka ‘yan bindiga 2 tare da kwato bindiga kirar Ak 47 guda daya, bindiga kirar gida guda daya alburusai masu tsayin 19.7.62mm na musamman baburan hawa guda 3 dai dai sauran muggana makamai.
A halin yanzu dai dakarun sojin na cigaba da bincikar sojojin da suka bata tare da kokarin bankado da maboyar ‘yan ta’addan.
Idan dai za’a iya tunawa Jaridar PRNigeria Hausa ta rawaito cewa dakarun rundunar Sojin bataliya ta 93 sun yi batan dabo, tun bayan suka kai wani sumamen aiki ga maboyar ‘Yan Ta’adda a kauyen Tati dake karamar hukuma Takum ta Jihar Taraba a yammacin Talata.
By PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 35 minutes 46 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 17 minutes 11 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com