Daidai lokacin da Kungiyar Daliban Jami’oin Nijeriya Ta NANs ke gudanar da zanga zangar kin jinin yajin aikin kungiyar ASUU, Hukumar dake lura da jami’oin kasar ta NUC ta bawa jami’oi 12 masu zaman kansu lasisin gudanarwa.
A kalla dalibai dubu 3 dake gudanar da karatu a jami’oin gwamnatin kasar suka tare manayan hanyoyi a Nijeriya tare da dakatar da zirga-zirgar ababa hawa a jami’ar Nsukka dake jihar Enugu a kudancin Nijeriya saboda yajin aikin na ASUU.
Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalaye da rubuce-rubuce kamar “ Muddin ba’a dakatar da yajin aikin ASUU ba, to babu zaben Fidda Gwani na Jam’iyyun Siyasa” “ mung aji da zama a gida” “ ya kamata Gwamnatin tarayya ta sasanta da ASUU, “Muna so Mu Koma makaranta.
Sai dai ana tsaka da wannan dambarwa Ministan Ilimin kasar Malam Adamu Adamu, ya gabatar da lasisin bude wasu sabbin jami’oi masu zaman kan su a kasar.
Sabbin jami’oin da aka mikawa lasisin sun hadar da Pen resources University a jihar Gombe; Al-ansar university a Garin maidugurin Jihar Borno: sai Margeret Lawrence University Galilee dake jihar Delta da kuma Khalifa Isiyaku Rabiu University, a Jihar Kano.
Read Also:
Sauran sun hadar da Sport University, dake Idumuje a jihar Delta sai Baba Ahmad university a jihar Kano sai kuma Saisa university of medical Sciences and technology, a jihar Sokoto da kuma Nigerian British University, dake Asa, a jihar Abia.
Akwai kuma Peter University, dake Achina/Onneh a jihar Aambra; sia Newgate University, Minna” Europena University of Nigeria, dake Duboyi a babban birnin tarayya Abuja sai kuma Northwest University Sokoto dake Jihar Sokoto.
Da yake jawabi a yayin taron mika lasisin ministan ilimin yace, duk cewa adadin jami’oin ka iya yin yawa amma akwai bukatar a samar da Karin jami’o’I a kasar.
“Gwamnati nada masaniya kan bukatarsamar da cigaba ga al’umma, sanina cewa dukkan kasashen da suka cigaba kuma ake lallaon su matsayin kasashe mafi daraja to sun kula da jami’o’in su gani da lura da yawan al’ummar su.
Yakuma ce sabbin jami’o’in zasu kasance suna da alaka da Tsuffin jami’o’in kasar a fannin koyo da koyarwa bisa jagorancin hukumar dake lura dasu ta NUC.
Ya bukaci masu mamallaka jami’oin dasu cigaba da samar da kudade domin inganta makarantun ta hanyar samar da kayan koyo da koyar da kuma baiwa jami’o’in damar karbuwa.
Daga bisani Babban sakataren hukumar dake lura da jami’oin kasar ta NUC Farfesa Abubakar Rasheed ya yabada kokarin wadanda suka samar da jami’o’in a Nijeriya.
By PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 17 minutes 21 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 13 hours 58 minutes 46 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com