Shalkwatar Tsaron Nijeriya (DHQ)  Ta Sami Nasarar Cafke Maharan Cocin Garin Owo a Jihar Ondo.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Manjo-Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a yayin wani taron tattaunawa da shugabannin kafafen yada labarai a shalkwatar tsaron da ke Abuja.

Manjo-Janar Irabor ya ce sojoji sun kama wadanda ake zargin ne tare da hadin gwiwar wasu hukumomin tsaro.

Idan za’a iya tunawa a ranar Lahadi 5 ga watan Yuni PRNigeria ta ruwaito cewa wasu ’yan bindiga sunyi dira mikiya cocin St. Francis Xavier da ke garin Owo a jihar Ondo dake Kudu maso Yammacin Najeriya.

Nan kuma babu bata lokaci suka buda wuta kan masu ibada inda suka kashe mutum 40 tare da jikkata wasu da dama.

Wannan lamari ya tayar da ya mutsi a tsakanin mabiya addinai, inda kowane bangare ke tayar da jijiyoyin wuya a kokarin kare addininsa.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 10 hours 40 minutes 12 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 12 hours 21 minutes 37 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com