Home SIYASA Goyon Bayan PDP Nasara a 2023, Jihadi ne – Dan Takarar Gwamnan...

Goyon Bayan PDP Nasara a 2023, Jihadi ne – Dan Takarar Gwamnan Katsina

Goyon Bayan PDP Nasara a 2023, Jihadi ne – Dan Takarar Gwamnan Katsina

 

SIYASA – Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Katsina a zaben 2023, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya ce goyon bayan jam’iyyarsa ta lashe zabe ya wuce siyasa, yana mai cewa ” jihadi ne “. .

Lado ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina lokacin da ya karbi bakuncin wasu jam’iyyun siyasa da suka koma PDP a karamar hukumar Safana ta jihar.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa da tarin masu sauya sheka a jihar, zai lashe zaben da gagarumin rinjaye.

“A nan Katsina, ba mu da rarrabuwar kawuna a PDP. Na yi takara da wasu uku, amma duk muna tare yanzu. Daya daga cikinsu shi ne abokin takarara a yanzu, dayan kuma yana neman kujerar majalisar tarayya.

“Na karshe kuma, koyaushe yana tare da mu, kuma duk abin da muke yi, muna tuntubar shi kuma yana ba da shawara mai mahimmanci,” in ji shi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp