Tinubu ba ya Nan Yayin Da ‘Yan Takarar Shugaban Kasa sun Shirya Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Tinubu ba ya Nan Yayin Da ‘Yan Takarar Shugaban Kasa sun Shirya Sa Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya

 

SIYASA – Wasu ‘yan takarar shugaban kasa da shugabannin jam’iyyun siyasa 18 da suka yi wa rajista sun fara isa cibiyar taron kasa da kasa (ICC) domin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kasa gabanin babban zabe na 2023.

Kwamitin zaman lafiya na kasa karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar da Bishop Matthew Hassan Kukah ne suka shirya taron.

An kirkiro shirin ne a shekarar 2014 domin mayar da martani ga barazanar da ke kunno kai a babban zaben shekarar 2015.

‘Yan takarar da suka halarci bikin da ake shirin farawa sun hada da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Kashim Shettima wanda ke wakiltar abokin takararsa, Bola Ahmed Tinubu; ‘Yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Action Alliance (AA) Omoleye Sowore da takwaransa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwanwaso.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullah Adamu, shi ma yana kan kujerar domin gudanar da taron.

Cikakkun bayanai anjima…

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 17 hours 45 minutes 50 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 19 hours 27 minutes 15 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com