‘Yan Bindiga: An Ceto Sauran Fasinjojin Jirgin Kaduna zuwa Abuja da Suka Rage Hannun ‘Yan Fashin Daji

Rahotanni daga Nijeriya na bayyana cewa An sako dukkan fasinjojin da suka rage a hannun wadanda ke garkuwa da su bayan da aka sace su a watan Maris na shekarar 2022 a cikin wani jirgin kasan da ke kan hanyar zuwa Kaduna daga birnin tarayya Abuja.
Wannan dai na kunshe ta cikin wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta hannun sakataren wani kwamitin ma’aikatar tsaron Najeriya CDSAC Farfesa Usman Yusuf ya fitar a ranar ranar Laraba, wadda take da yammacin ranar laraba dakarun soji sun sami nasarar ce sauran mutane da suka rage hannun masu garkuwar.
“Ina mai farin cikin sanar da kasa da ma duniya cewa da misalin karfe 4 na yammacin yau Laraba 5 ga watan Oktoba 2022, kwamitin mutum bakwai da hafsan hafsoshin dakarun tsaron kasa Janar L. E. O. Irabor ya sami nasarar ceto sauran fasinjoji 23 da suka rage a hannun ‘yan ta’adda na Boko Haram bayan da suka kai hari kan jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris na 2022.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan kasar na cike da godiya ga sojojin Najeriya a karkashin jagorancin hafsan hafsoshin sojojin kasar, wanda shi ne ya jagoranci aikin daga farkonsa har zuwa karshe. Haka ma, sauran hukumomin tsaro da ma’aikatar sufuri duka sun taimaka gaya wajen nasarar da muka samu a wannan aikin.”
Sai dai kawo yanzu babu rahotannin inda aka kai fasinjojin da aka sako, ko yadda aka iya karbo su daga hannun ‘yan Boko Haram din da suka yi garkuwa da su na tsawon fiye da wata shida.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 11 minutes 35 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 53 minutes 0 second

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com