Gwamnatin Najeriya ta ayyana Litinin 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu don murnar bikin Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (S.A.W).
Wannan na kunshe ta cikin wata Sanarwar da Babban Sakataren ma’aikatar cikin gida Dr. Shuaib Belgore ya fitar a madadin Minista cikin gida Ra’uf Aregbesola wadda tayi kira ga ‘yan Najeriya musamman al’ummar Musulmi su guji ayyukan tada tarzoma da rashin bin doka da sauran ayyukan laifi.
Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya sanar da haka a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya ya taya al’ummar Musulmi a gida da ƙetare murnar sake ganin wannan biki na bana.
Read Also:
Daga bisani ya gargaɗi duk ‘yan kasar da su rungumi son juna da haƙuri da jure zama da juna da jimiri waɗanda na cikin jerin halayen fiyayyen halitta Annabi Muhammadu, inda ya ƙara da cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro da zaman tare a Najeriya.
Da yake kira a dakatar da duk wasu halaye da za su kawo rarrabuwar kai a faɗin ƙasar, ministan ya kuma buƙaci duk ‘yan Najeriya da kuma musamman matasa su rungumi ɗabi’un aiki tuƙuru da halayyar zaman ga ‘yan’uwansu bil’adama ba tare da la’akari da bambancin addini ko aƙida ko rukunin jama’a da ƙabila ba.
Aregbesola ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya su kasance masu tunanin yanayin tsaro, kuma su kai rahoton duk wani mutum ko aikace-aikacen da ba su amince da take-takensu ga hukumomin tsaro mafi kusa.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 53 minutes 39 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 35 minutes 4 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com