Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Justice Olukayode Ariwoola a matsayin babban alkalin alkalan Najeriya (CJN).
Bikin rantsuwar da ya gudana gabanin fara taron majalisar zartarwa ta tarayya na mako, (FEC), ya samu halartar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, da gwamnonin jihohin Oyo da Ondo, Seyi Makinde da Rotimi Akeredolu.
sai kuma Sauran alkalan kotun kolin Najeriya wadanda a matsayin wadanda suka halarci bikin; Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha; Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Rtd).
Read Also:
Sauran sun hadar da ministocin da suka shigo domin halartar taron majalisar na mako, ciki har da Hadi Sirika (Aviation); Olorunnimbe Mamora (Kimiyya, Fasaha); Chris Ngige (Kwadago da Nagartar Aiki); Abubakar Malami (Ministan shari’a, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya); Niyi Adebayo (Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari); Babatunde Fashola (Ayyuka da Gidaje); Abubakar Aliyu (Makamashi) da sauransu.
Da yake zantawa da manema labarai bayan rantsar da shi, Mai shari’a Ariwoola ya yi kira ga ‘yan siyasa a kasar nan da su kyale bangaren shari’a ya yi aiki yadda ya kamata ganin yadda zaben 2023 ke gabatowa yayin da ya yi alkawarin kawo gyara a kotun koli.
A nasa bangaren, gwamna Seyi Makinde ya bayyana godiya a madadin jama’a da gwamnatin jihar Oyo ga shugaban.
A halin da ake ciki, majalisar ta yi shiru na minti daya domin karrama tsohon ministan ayyuka na musamman kuma shugaban jam’iyyar PDP, Cif Vincent Ogbulafor, wanda ya rasu kwanan nan.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 43 minutes 5 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 24 minutes 30 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com