Kasar Amurka tayi watsi da duk wani yunkuri na sake shiga tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran nan kusa, abinda ake gani zai dakushe fatan da ake da shi na kulla sabuwar yarjejeniya akan wadda akayi a shekarar 2015.
Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar John Kirby yace ba wai basa bukatar ganin an aiwatar da yarjejeniyar bace, sai dai a halin yanzu basu ga wata hanyar kulla ta ba a nan kusa.
Kirby yace abinda ke gabansu yanzu shine daukar mataki akan kasar Iran saboda yadda take murkushe masu zanga zangar adawa da mutuwar Mahsa Amini, matashiyar da aka samu da laifin kin sanya hijabi a ranar 16 ga watan Satumba.
Read Also:
Mai magana da yawun fadar shugaban yace har yanzu shugaba Joe Biden na nan kan matsayinsa cewar ba zai taba barin kasar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.
Zanga zanga ta barke a sassan kasar tun bayan mutuwar Amini, abinda ya kaiga arangama tsakanin Yan Sanda da masu adawa da matakin da jami’an tsaro suka dauka, abinda ya kaiga mutuwar mutane sama da 100 da kuma kama wasu sama da 100 da tuni aka gurfanar a gaban shari’a.
Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya zargi Amurka da kawayenta da tinzira masu zanga zangar domin jefa kasar cikin tashin hankali, yayin da kasashen Turai suka amince da wani shirin kakabawa kasar takunkumi akan lamarin.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 40 minutes 28 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 21 minutes 53 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com