Kungiyar malaman Jami’oin Nijeriya ta (ASUU) ta dakatar da yajin aikin data kwashe tsawon watannin ta yi bisa wasu dalilai, kamar yadda kwamitin amintattun kungiyar ya shaidawa manema labarai a safiyar juma’a.
Kungiyar ta yanke hukuncin janye yajin aikin ne bayan wata ganawa da shuwagabannin suka fara gudanarwa tun daga daren alhamis zuwa wayewar garin juma’a.
Read Also:
Kungiyar ta kira taron gawanar ne domin yanke matakin ta na karshe bayan da mambobin ta na jihohi suka gana kan hukuncin kotun daukaka kara a makon daya gabata.
Kotun daukaka kara ta umarci kungiyar ASUU da ta dakatar da yajin aikin kafin a saurari daukaka karar da ta yanke, inda ta umarci malam su koma bakin aiki.
Mambobin kwamitin zartawa na kungiyar na kasa, wadanda suka hadar da shuwagabannin kungiyar na jihohin dana kasa ne suka halarci taron a sakatariyar kungiyar ta ASUU dake birnin tarayya Abuja.
Kungiyar malaman jami’oin ta ASUU ta tsunduma yajin aikin ne tun a 14 ga watan fabrerun 2022.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 28 minutes 25 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 9 minutes 50 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com