Ana Zanga-Zanga kan Tabarbarewar Tattalin Arziki A Tunisia

Dubu Dubatar ‘yan kasar Tunisiya ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Tunis a jiya asabar don yin tir da manufofin shugaba Kais Sa’id, wanda suke zargin shi ne ke da alhakin tabarbarewar tattalin arzikin kasar, wanda ke fuskantar matsalar karancin kayan masarufi da hauhawar farashin kayayyaki.

A karkashin jagorancin jam’iyyar National Salvation Front, gamayyar jam’iyyun adawa masu zanga-zangar sun tsallaka manyan titunan babban birnin Tunisiya, suna kira da shugaban ya yi murabus.

Wannan zanga-zangar tana nuna fushin halin da ake ciki a Tunisiya karkashin Kais Saied da kuma kira da  ya yi murabus, kamar yada tsohon Fira Minista Ali Laaraydh, mataimakin shugaban Ennahdha, ya shaida wa manema labarai.

A dai-dai lokacin da jama’a ke gudanar da wannan zanga-zanga ,asusun ba da lamuni na duniya IMF ya cimma yarjejeniya da gwamnatin kasar ta Tunisia wadda za ta bada damar biyan dala biliyan 1.9 yayin da Tunisia ke fama da matsananciyar matsalar tattalin arziki.

PRNigeria Hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 15 minutes 7 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 56 minutes 33 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com