Sarki Charles na III ya tabbatar da Rishi Sunak matsayin Firaministan Birtaniya, kuma bayan tabbatarwar ya sha alwashin gyara kurakuran da aka tafka wadanda suka kai kasar ga fadawa halin matsananciyar matsalar tattalin arziki.
Sunak mabiyin addinin Hindu mai shekaru 42 wanda Sarki Charles na 3 ya tabbatar da shi a matsayin Firaminista da misalin karfe 11 da mintuna 15 na safiyar yau talata, shi ne Firaminista na 3 da kasar ta gani cikin shekarar nan.
Wannan ne dai nadi na farko da Sarki Charles na 3 ya jagoranta la’akari da cewa Sarauniya Elizabeth ce ta tabbatar da nadin Liz Truss kwanaki kalilan gabanin mutuwarta.
Read Also:
Jim kadan bayan tabbatar da shi, Rishi Sunak ya ce aiki na farko da zai sanya a gaba shi ne samar da sauye-sauye don gyara ga kura-kuren da aka tafka cikin makwanni 7 na mulkinta Truss lamarin da ya durkusar da tattalin arziki.
A cewarsa baya zargin Truss kuma matakan da ta dauka ba gazawa ba ce, haka zalika bada mummunar manufa ta samar da sauye-sauyen da suka illa ga tattalin arziki ba, hasalima tsari ne mai kyau sai dai sun juye zuwa matsala ne saboda halin da Duniya ke ciki.
Yayin jawabinta na ban kwana Truss ta yiwa Sunak fatan alkhairi da kuma fatar warwarewar matsalolin da suka dabaibaye sashen tattalin arzikin kasar wanda ya jefa jama’a a halin matsin tattalin arziki.
PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 38 minutes 55 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 20 minutes 20 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com