Watanni biyu bayan samun nasarar lashe zaben shugaban kasar Kenya William Ruto ya rantsar da kunshin majalisar ministocin a ranar Alhamis.
Ministocin guda 12 an rantsar dasu ne domin tunkarar matsalolin da suka addabi kasar da suka hada da tsadar rayuwa da kuma sauran batutuwa suka shafi tattalin Arziki a kasar dake gabashin nahiyar Afirka, wanda wannan na cikin alkawurran da Ruto ya dauka yayin yakin neman zaben sa.
Sai dai kuma ana kallon sabuwar majalisar da Ruto ya kafa bata cimma daidaiton jinsi ba kamar yadda ya alkawurta tun a yakin neman zaben nasa, inda aka bayyana sunayen mata 7 kawai.
Tsohon mataimakain shugaban kasar kuma tsohon dan adawar Raila Odinga daya marawa Ruto baya Musalia Mudavadi ya zama sabon sakataren firaministan kasar da aka kirkiro.
Read Also:
Sai kuma Alfred tsohon gwamna wanda jam’iyyar sa ta goyi bayan Ruto shi ne zai jagoranci ma’aikatar harkokin wajen kasar.
Kithure Kindiki, wand ana cikin lauyoyin da suka kare zaben Ruto a watan Agusta, shine zai jagoranci ma’aikatar cikin gida mai karfi.
Kindiki shine wanda ya wakilci Ruto a shari’ar da ake yi masa a Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa dake birnin Hague lokacin da aka zrge shi da hannu wajen kitsa tarzomar da ta biyo bayan zaben 2007- 2008 wanda yayi sanadin mutuwar mutane akall 1,100 tare da raba sama da 600,000 da muhallansu.
Sai kuma ma’ajin kasar da Njuguna Ndung’u zai jagoranta, wanda shine tsohon gwamnan babban bankin kasar.
PRNigeria Hausa
(AFRICA NEWS)
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 59 minutes 10 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 40 minutes 35 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com