Rahotanni na bayyana cewa ana cigaba da laluben wadanda suka nutse a ruwa bayan ruftawar wata tsohuwar gada a kasar India, abinda ake ganin ya shafi akalla mutane 130.
Tun da fari dai ‘Yan sanda a kasar sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da 130, lokacin da wata gada da ta kwashe shekaru sama da 100 ana amfani da ita ta rushe, abinda ya sanya wasu da dama fadawa ruwa.
Daya daga cikin manyan jami’an ‘yan sanda a kasar ta India, Ashok Kumar Yadav, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar zuwa wayewar garin Litinin din nan, adadin mutane 132 aka tabbatar da mutuwarsu bayan rushewar gadar da ta kwashe kusan shekaru 150 ana amfani da ita.
Read Also:
Ministan dake kula da Yammacin jihar Gujerat, Brijesh Merja yace kuma anyi nasarar ceto mutane sama da 80 da ransu.
Mahukunta sun ce akalla mutane kusan 500 ke kan gadar lokacin da ta rufta sakamakon sakewar da robobin dake rike da ita suka yi, cikin su harda mata da yara.
Ita dai wannan gadar ba’a dade da kammala gyaranta ba, tana garin Morbi ne dake da nisan kilomita 200 daga Ahmedabad a Jihar Yammacin Gujerat.
Kafofin yada labaran kasar sun ce mutanen da suka taru akan gadar suna gudanar da ibada ne akan kogin Machchhu, yayin da wasu kafofi suka nuna hotunan bidiyon da ake bayyana cewar na hadarin ne dauke da mutanen dake kokarin yin fito domin tsira da rayukansu.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 16 minutes 41 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 58 minutes 6 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com