Ana Zanga-Zanga A Ghana Saboda Tsadar Rayuwa

Daruruwan ‘yan Ghana sun fantsama kan titunan birnin Accra, suna kira ga shugaban kasar, Nana Akufo-Addo da ya yi murabus sakamakon tsadar rayuwa da kuma gazawar gwamnatinsa wajen tunkarar matsalar tattalin ariki.

A makon da ya gabata ne shugaba Akufo-Addo ya roki ‘yan kasar da su amince da shirinsa na karbo bashi daga Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF duk da cewa, wani lokaci a can baya, ya taba yi wa ‘yan kasar alkawarin cewa, ba za su ciyo basuka ba.

Yanzu haka dai matsalar tattalin arziki ta shafi kusan kowanne bangare na al’ummar kasar ta Ghana da suka hada da masu hali da talakawa.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka zanta da manema labarai sun ce, babu abin da suke son gani face shugaban kasar da wasu mukarrabansa su yi murabus saboda sun gaji da yadda kasar ke tafiya a cewarsu.

Ghana dai na neman rancen Dala biliyan 3 daga Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF domin shawo kan matsalar hau-hawan farashi da kashi 37  da kuma magance zubewar darajar kudin kasar na Cedi.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 9 hours 39 minutes 23 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 11 hours 20 minutes 48 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com