Manoma Afrika da Asiya zasu Rabauta da Tallafin Dala biliyan 1.4

An bukaci kasashe masu karfin mawadata da su biya diyar kudade ga takwarorin su matalauta, sakamakon yadda suka haddasa aukuwar musibu masu nasaba da sauyin yanayi a kasashen nasu.

Wanan na zuwa ne bayan bude taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya mai take COP27 dake gudana a kasar Masar.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya mai tada hankali ya ce, shekaru takwas da suka shude na baya-bayan nan, sun zama mafi samun dumamar yanayi a tarihi, inda aka samu tumbatsar tekuna, narkewar tsaunukan kankara , tsananin zafi da dai sauran ibtila’o’in da ke nuni da sauyin yanayi.

Sakatere Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya ce, a daidai lokacin da aka bude taron  na COP27, wannan doran duniyar da muke rayuwa a kai, na aikewa da mummunan sako.

A ‘yan watanni da ssuka gabata, ambaliyar ruwa ta yi barna sosai a kasashe irinsu Pakistan da Najeriya, sannan matsalar fari ta yi kamari a nahiyar Afrika da Amurka, yayin da kuma guguwa ta yi shara a yankin Caribbean, inda kuma aka samu wani irin zafi mai tsanani da ba a taba gani ba a nahiyoyi uku na duniya.

Taron na COP27 da ke gudana a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh da ke kasar Masar, na zuwa ne a daidai lokacin da ake gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine, al’amarin da ya haddasa hau-hawan farashin kayyaki a sassan duniya.

Taron na bana zai fi mayar da hankali ne kan yadda za a tara kudaden tunkarar matsalar ta sauyin yanayi.

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 15 hours 5 minutes 36 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 16 hours 47 minutes 1 second

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com