Home DUNIYA Iran ta Kera Sabon Samfurin Makami Mai Linzami

Iran ta Kera Sabon Samfurin Makami Mai Linzami

Iran ta ce ta kera wani makami mai linzami mai matsanancin gudu da ka iya ratsa duk wani tsarin tsaro da aka shimfida, kamar yadda babban kwamandan rundunar juyin juye hali ta kasar Amirali Hajizadeh ya bayyana a yau Alhamis.

Wannan shu’umin makami mai linzami, kamar sauran makamai masu cin dogon zango, yana da gudun da ya ninka sauti har sau 5.

Hajizadeh ya ce an yi wannan makami ne don iya waske duk wani tsari na tsaron makami mai linzami, inda ya kara da cewa zai dau gwamman shekaru kafin a samar da wani tsarin tsaro da zai dakile shi.

Wannan sanarwar na zuwa ne kwanaki bayan da iran ta amsa zargin cewa ita ta bai wa Rasha jirage marasa matuka, amma ta musanta cewa ta bada jiragen ne bayan mamayar Ukraine.

Akasin makami mai cin dogon zango, wannan makami mai linzami yana tafiya ne a kasa kasa da sararin samaniya, lamarin da ya sa yake iya kai wa ga inda aka harba shi da wuri.

Gwajin irin wannan makami da Korea ta Arewa ta yi a shekarar da ta gabata ya haddasa damuwa a kan rige rigen samun makamancin makamin.

A yayin da kasashe kamar su Amurka suka samar da na’urori da ke bada kariya ga makami mai linzami da ke cin dogon zango, taka wa wannan shu’umin makami birki na da matukar wahala.

tushe RFI

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp