Home General Dakarun Sojin Nijeriya Sun yi Barin wuta kan ‘yan Ta’adda a jihar...

Dakarun Sojin Nijeriya Sun yi Barin wuta kan ‘yan Ta’adda a jihar Kaduna

Rundunar sojin saman Najeriya ta kai wani samame ta sama a kan wasu gungun ƴan bindiga da aka gano a wasu wuraren da ke cikin wasu kananan hukumomin Kaduna, inda suka hallaka da dama da ga cikin su.

wannan na kunshe ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan tsaro da harkokin cikin , Samuel Aruwan, ya fitar aka raba ga manema labarai.

Ya ce an yi luguden wutar a kan ƴan ta’addan ne a yankin Kawara da ke karamar hukumar Igabi a wuraren da ‘yan bindigar samu maɓoya.

“An tabbatar da kashe ‘yan bindiga a harin na jirgin sama kuma wasu da aka yi garkuwa da su sun samu tserewa daga yankin gaba daya, kamar yadda wasu majiyoyi masu sahihanci na suka tabbatar.

 “Hakazalika, a Walawa, karamar hukumar Giwa, an kai hari a wani wuri da aka yi nasarar gano wa. A karamar hukumar Chikun, an gudanar da aikin sa ido a kan Faka, Kangon Kadi, Damba, Ungwan Turai, Galbi, Gwagwada da kewaye. An ga ‘yan ta’adda a nisan kilomita 4 daga Arewa maso Yamma da Godani, kuma duk an kashe su,” inji shi.  Aruwan ya ci gaba da cewa a Kuduru, an ga inda ‘yan ta’addan suka kai hari da rokoki.

Ya ce a karamar hukumar Igabi, an gudanar da ayyuka a kan Riyawa, Alhaji Isiaka, Rima, Riyawa, Rumana, Ungwan Liman, Mai Gishiri da kuma yankin filin jirgin sama na Kaduna ba tare da sojojin sun raunata ba.

Ya kuma kara da cewa an samu irin wannan lamarin a Sabon Birnin, Anaba, Malumi, Wusono da Kerawa.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp