Buhari ya kaddamar da fara gina Shalkwatar ECOWAS a Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da tubalin ginin sabuwar hedikwatar Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS a Abuja babban birnin ƙasar.
Shugabannin ƙasar Guinea Bissau Umaro Embaló, da na Saliyo Julius Maada Bio, da Shugaban Ecowas Omar Alieu Touray, da Jakadan China a Najeriya Cui Jianchun, su ne suka taya Buhari saka ɗambar ginin a yau Lahadi.
Ana sa ran kammala sabuwar hedikwatsar a shekara ta 2025.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana cewa hamshaƙin ginin, wanda gwamnatin China ta samar da kuɗin ginawa, zai ƙarfafa zumunci a tsakanin ƙasashen Afirka.
Ginin zai kuma wakilci al’ummar Afirka ta Yamma mutum miliyan 380 sannan zai kasance matsuguni ga manyan cibiyoyin Ecowas uku, ciki har da ginin hukumar gudanarwar ƙungiyar da Kotun Ecowas, har ma da Majalisar Dokokin Ecowas.
A gefe guda kuma, shugabanin mambobin ƙungiyar na gudanar da taro karo na 62.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 31 minutes 26 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 12 minutes 51 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com