Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya rattaba hannu a Kasafin kudin Shekara ta 2023 wanda Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta Amince da shi.
Gwamnan ya Sanya hannun ne yayin taron Majalisar Zartarwar ta Jihar Kano wanda ya gudana a dakin taron majalisar dake gidan gwamnatin jiha.
Gwamna Ganduje ya yabawa yan majalisar bisa yadda sukai aikin kasafin kudin ba tare da bata lokaci ba, Wanda hakan zai baiwa Gwamnatin damar fara amfani da kasafin kudin a farkon sabuwar Shekara tunda ya Zama doka.
Gwamnan Ganduje yace bai yi mamakin yadda yan Majalisar suka kammala aikin nasu da wuri ba, Inda yace zai tabbatar an yi aikin da kasafin kudin kamar yadda majalisar ta amince da shi.
Ganduje ya yi alkawarin Cigaba da baiwa Majalisar yancin cin gashin kanta, ba tare da tsoma baki a harkokin aikin Majalisar ba.
Ya Kuma yaba da yadda Majalisar ta Gudanar da taron Jin ra’ayoyin al’umma akan kasafin, Inda ya bada tabbacin Kasafin kudin zai fi mai da hankali wajen kammala aiyukan da suka fara don gudun barin bashi mai yawa ga gwamnati mai zuwa, Inda yace kasafin kudin ya samu kari daga Sama da Naira Biliyan 23.
tun da fari Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Kano Hamisu Ibrahim Chidari yace sun Sami nasarar kammala aikin nasu ne akan lokaci Saboda yadda Gwamnan ya gabatar musu da daftarin Kasafin akan Lokaci.
Chidari yace Kuma dukkanin Shugabannin Ma’aikatu da Hukumomin Gwamnatin Jihar Kano sun bayar da duk wani hadin Kai ga kwamitocin Majalisar wanda hakan ya taimaka wajen Samun nasarar aikin kasafin kudin kamar yadda doka ta basu dama.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 38 minutes 16 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 19 minutes 41 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com