Kamfanin dakon wutar lantarki na Nijeriya (TCN) ya bayyana cewa babu gudu ba ja da baya kan yunkurin s ana ruguje gidaje dubu 1 da aka gin aba bisa ka’ida ba karkashi turakun wayoyin lanatarki a jihar kano.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin ke musanta cewa gidajen da aka ware domin rugujewa sun haura dubu 20, inda kamfanin yace tun daga dan’agundi zuwa kumbotso gidaje da gine-gine da ba kamala ba basu wuce 100 ba.
Mataimakin Babban daraktan kamfanin, Alh. Muhammad Kamaru Bello, yace layin wayar wutar lantarki guda daya ne ya kawo wuta jihar kano daga jihar Kaduna wanda kuma aka hada shi tsahon shekaru 50 da suka gabata.
Sai dai mafi yawa daga cikin su an gaza biyan su hakkokin su, kuma hakn ya biyo bayan biyan daiyyar naira biliyan 1.5 yayin da kano ta biya naira miliyan 500 a tashar wutar ta Dan’Agundi da tashar rimin zakara.
Yace tashar wutar ta Dan’aAgundi an samar da ita ne shekaru hamsim da suka gabata, wadda take bada megawatts 80, amma zuwa yamzun tana samar da sama da megawatt 280 wannan ne ya sanya za’a gudanar da aikin.
Ya bayyana cewa dukkan wasu shirye-shirye wajen gudanar da aikin nan da kwanaki masu zuwa, za’a fara aikin sake gina layukan samar da wutar lantarki na biyu daga kano zuwa kaduna, yace babu gudu babu ja da baya.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 18 hours 5 minutes 40 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 19 hours 47 minutes 5 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com