Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi gargadi wadanda ke kokarin kawo cikas ga zabukan da ake shirin gudanarwa cikin shekara ta 2023 a kasar cewa lalle za su hadu da fushin doka.
Shugaba Buhari ya yi wannan gargadi ne a jawabin da ya gabatar wa al’ummar kasar dangane da shiga sabuwar shekara ta 2023, yana mai kira ga illahirin ‘yan Najeriya da su tabbatar da wadannan zabuka sun gudana a cikin yanayi na tsari, ‘yanci da kuma mutunta doka.
Buhari ya ce watannin da ke gaba na da matukar muhimmanci ga gwamnatinsa, musamman a fannoni guda uku da suka hadar da tsaro, tattalin arziki da kuma ci gaba da yaki da rashawa a duk fadin kasar.
A wani bangare na jawabinsa, Muhammadu Buhari ya ce ya zama wajibi ga ‘yan Najeriya su tabbatar da cewa ‘yan siyasa ba su yi amfani da su domin tayar da fitina a lokacin wadannan zabuka da take ba.
Shugaban ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da ya ce ya samu a cikin shekaru 7 da suka gabata, sannan ya ce yana murna ga wadanda ke yaba wa kokarin da ya yi da ma wadanda ke sukar salon mulkinsa.