Mai Martaba sarkin katsina ya nada shugaban hukumar NIA matsayin Sardaunan Katsina.

Mai Martaba sarkin katsina ya nada shugaban hukumar NIA Ahmed Rufa’I matsayin Sardaunan katsina.
An nada babban daraktan hukumar tattara bayanan sirri Amb. Ahmed Rufa’I Abubakar matsayin sardaunan Katsina.
Mai martaba sarkin katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya nada shugaban hukumar ta NIA matsayin sardaunan na katsina a ranar Asabar.
Taron nadin sarautar ya sami halartar manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya, cikin su har da shugaban majalisar Dattawan Nijeriya, Ahmed Lawan.
Amb. Ahmed Rufa’I ya fito daga zuri’ar Muhammad Maude, Jarumi kuma sadauki, wanda tarihi ya nuna shine wanda ya samar da Unguwar Maude dake katsina a cikin a kashin farko cikin ukun karni na 19.
An gudanar da nadin ne a fadar mai martaba sarkin katsina, cikin nutsuwa da annashuwa, taron ya sami halartar manyan baki daga ciki da wajen kasar.
Da yake jawabi ga dimin jama’a da suka sami halartar taron nadin mai martaba sarkin Katsina, yace nadin sarautar sardaunar da aka yiwa shugaban hukumar ta NIA, ya nuna godiya da irin kyakkyawar hidimar da ya yiwa katsina, nijeriya da kuma tsarin kasa da kasa, gami da jajircewa wajen aiki tukuru da rikon amana.
Sarkin yayi kira ga sauran masu rike da madafun iko a Nijeriya da su yi aiki da aminci tare da sauke nauyin dake kan su.
Sarkin ya bayyana kabilanci da nuna banbancin addinin matsayin abinda ke kawo tasgaro ga hadin kan kasa, inda ya bukaci ‘yan kasar dasu kawar da su domin samun cigaban kasar.
Sabon sardaunan katsina, Ahmad Rufa’I Abubakaya sami lambobin yabo da dama. Suka hadar da DGNIA bisa kwazo sai kuma lambar yabo ta l’Ordre National de la Republique du Niger wanda shugaban jamhuriyyar Nijar ya damka masa, sai kuma lambar yabo ta CFR, wadda shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bashi, da dai sauran manyan lambobin girmamawa daya samu

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 17 hours 7 minutes 3 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 18 hours 48 minutes 28 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com