Kamfanonin tsaron Najeriya ta bai wa kwangilar tsaron bututan man fetur sun kama jiragen ruwa da mota maƙare da man da hukumomi suka ce na sata ne a yankin Neja-Delta da ke kudancin ƙasar.
Wata sanarwa da kamfanin mai na kasar, NNPC Limited, ya fitar a ranar Asabar ta tabbatar mutum huɗu aka kama yayin samamen.
Read Also:
Kamfanin ya samu rahoton sirri game da ayyukan mutanen tun a ranar 22 ga watan Disamba.
Dakarun tsaro sun isa wurin kuma suka tarar da su suna jigilar man ta ɓarauniyar hanya tare da tace gas a wata matata da ke Agge.
Tuni hukumomi suka ƙona jirgin da kayan da yake ɗauke da shi.
PRNigeria hausa