Wani harin mayakan Boko Haram ya yi Sanadiyyar Mayakan ISWAP.

‘Yan Ta’addan kungiyar Boko haram sun fatattaki Mayakan iswap tare da hallaka 35 daga cikin su.

Hare-haren da bangarorin ke ci gaba da kai wa a sansanonin juna wanda kwamandan Boko Haram, ABU UMAIMAH ko BAKOURA DORO ne suka jagoranci kai harin tare da Kwamandoji hudu da wasu mayaka da dama.

Harin da aka fara a Arewacin Kayowa da Toumbun Gini, a Arewa maso Gabashin tafkin Chadi, ya kai ga halaka mayakan ISWAP 35 yayin da wasu da dama suka jikkata.

Zagazola ya rawaito cewa, kwamandan kungiyar Boko Haram maras tausayi ya kuma kwace makamai masu tarin yawa daga hannun ‘yan ta’addar ISWAP, yayin da suka tsere daga sansanonin su.

Majiyar ta bayyana cewa wata babbar kasuwa ta ISWAP dake Toumbun Gini, yan kungiyar JAS ne suka karbe ta a halin yanzu.

Zagazola ya fahimci cewa ‘yan ta’addan da suka tsere abikan gabar tasu sun bi su ne ta kudancin Kangarwa da Dogon Chuku a karamar hukumar Baga.

A makonnin da suka gabata, Yan ta’addan na Boko Haram, sun yi mummunar barna a sansanonin ISWAP da ke dajin Sambisa da kuma yankin tafkin Chadi, lamarin da ya tilastawa ISWAP daukar matakan kariya.

Ko da a ranar 31 ga watan Disamba, an kai hare-hare tsakanin bangarorin ISWAP da JAS da suka dauki tsawon sa’o’i 14 a yankunan Toumbum Allura da Kangar, inda aka kashe mayakan da dama.

Ya bayyana cewa ci gaba da kai hare-hare ya tilastawa mayakan na ISWAP gudanar da taro a Tumbun Murhu tare da manyan shugabannin ISWAP da suka hada da Abubakar Chad, Bashir Ukasha da Abul Kaka- Alias ​​Sa’ad.

Majiyar ta bayyana cewa, manyan batutuwan da aka tattauna a yayin taron su hadar da yadda kungiyarsu ta kasa kai wasu manyan hare-hare a lokacin bukuwan kirsimeti da sabuwar shekara kamar yadda aka tsara tun farko wanda ake dangantawa da fada da hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai kan sansanonin ta.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 20 minutes 44 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 2 minutes 9 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com