Kwankwaso yace zai ingata fannin Ilimi idan ya zama shugaban Nijeriya

Abuja – Dan takarar shugaban kasa a inuwar New Nigerian Peoples Party, Rabiu Kwankwaso, yace idan ya ci zabe, gwamnatinsa zata gina Azuzuwan karatu 500,000 ga yara kanana marasa galihu.

Kwankwaso ya dauki wannan alkawarin ne ranar Litinin a wurin kadammar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, (PCC), a birnin tarayya Abuja.

Haka nan Kwankwaso ya bayyana cewa gwamnatinsa zata tabbata manyan makarantun gaba da Sakandire sun kai matakin gogayya a duniya.

Kwankwaso yace “Bari na tuna mana cewa a shirye muke mu sauya bangaren ilimi domin mu inganta shi kuma kowa ya samu damar neman ilimi. Musamman zamu gina Azuzuwa 500,000 a sassan jihohin kasar nan.”

“Zamu zuba kananan yara sama da miliyan 20m dake gararamba a sabbin Azuzuwa domin muna da kudirin kawar da su daga yawo a Titunan Najeriya. Zamu maida duk wani Fam na neman gurbi da ɗaukar aiki kyauta.”

“Jarabawar gama Sakandire da ta share fagen shiga manyan makarantu kamar WAEC, NECO, NABTEB, NBIAS, JAMB da sauransu zamu maida su kyauta ga ‘yan Najeriya.”

Da yake tabo Jami’a, kwalejin fasaha da sauran manyan makarantun gaba da sakandire, tsohon gwamnan jihar Kano ya ci gaba da cewa:

“Zamu inganta tare da fadada jami’oi, kwalejojin fasaha, da baki daya kwalejojin mu na ilimi kuma mu daga darajarsu su kai matakin gogayya a duniya. SH

NNPP ta kaddamar da shafin tallafawa kamfen Kwankwaso

Bayan haka, jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ta kaddamar da bude shafin yanar gizo na hada kuɗi domin taimaka wa yakin neman zaben shugaban kasa.

PRNigeria hausa

 

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 35 minutes 53 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 17 minutes 18 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com