Shugaban hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON Zikrullah Kulle Hassan ya jagoranci tawagar masu ruwa da tsaki zuwa kasa mai tsarki domin kulla yarjejeniya da hukumomi daban-daban na kasar Saudiya a wani mataki na fara shirye-shiryen aikin hajjin bana.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar NAHCON ta fitar mai dauke da sa hanun mataimakin daraktar yada labanta Musa Uban Dawaki, inda yace manufar ziyar ita tattaunawa da masu ruwa da tsaki akan harkokin aikin Hajji dake kasar tare da kula yarjejeniya akan yadda aikin hajji 2023. zai guduna .
Rahotonni sun bayyana cewar tuni dai karamin ministan harkokin kasashen wajen Najeriya Ambasada Zubairu Dada ya sanya hannu a kan takaddar yarjejeniyar da aka cimma a kasa mai tsarki a madadin Najeriya.
Read Also:
A zantawarsa da manema labarai daga kasa maitarki kwamishinan hukumar mai kula da harkokin kudi da ma’aikata, Alhaji Nura Hassan Yakasai, ya ce hakan yana nufin kokarin da hukumar ke yi a karkashin jagorancin shugabanta Zikrullah Kulle Hassan na tabbatar da cewar aikin Hajjin 2023 ya zarta wadanda ake gudanarwa a baya cikin ikon Allah.
Sannan ya yi karin haske akan manufofin kulla yarjejeniyar da muhimmancin ta ga Najeriya.
Nura Hassan Yakasai, ya ce cikin ikon Allah shirin da NAHCON ke yi a wannan shekara ta nuna za’a samu nasara fiye da yadda ake gabatar shirin gudanar da aikin hajjin a shekaru baya.
Cikin tawagar akwai Karamin Ministan harkokin Kasashen waje na Najeriya Ambasada Zubairu Dada, da shugaban kwamitin harkokin kasashen waje a majalisar dattawa Sanata Adamu Bulkacuwa, sai shugaban kwamitin aikin hajji a majalisar wakilai ta tarayya Abubakar Hassan Na Laraba, kwamishinonin hukumar aikin hajjin gami da yan kwamitin gudanarwata.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 14 hours 45 minutes 0 second,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 26 minutes 25 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com