Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gargaɗi gwamnatocin ƙasashen ketare kan tsoma baki ko katsalanda a harkokin cikin gidan ƙasar musamman a lokutan zaɓe da ke tafe kasa da kwanaki 42.
Shugaban ya sanar da hakan ne lokacin da yake maraba da sabbin jakadun Switzerland da Sweden da Jamhuriyar Ireland da Thailand da Senegal da Sudan ta Kudu a fadar gwamnati.
Shugaban ya ce Najeriya tana aiki kafada-kafada da kungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas domin shawo kan matsalolin tsaro da bijiro da matakan tabbatar da zaɓe mai sahihanci ba tare da katsalanda ga kudin tsarin mulkin kasar ba.
Ko a shekarar da ta gabata sai dai shugaba Buhari ya yi irin wannan gargadi inda yake cewa burinsa shi ne ganin anyi sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali.
Wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar ta rawaito shugaba Buharin ya gargadin jakadun ketare kan su mayar da hankali kan abin da ya shafesu da dalilan turo su Najeriya, da kuma kawar da kai kan abubuwan da ba huruminsu ba ne.
Buhari ya ce babu shakka dole za a sa ido kan yada zaɓukan Najeriya za su kasance don haka fatansa shi ne ganin wakilan ƙasashen sun mayar da hankali wajen shirya yada ayyukansu zai kasance domin tabbatar da ganin komai ya tafi cikin kwanciyar hankali.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1239 days 12 hours 41 minutes 34 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1221 days 14 hours 22 minutes 59 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com