Home General Gobara ta kone shaguna 45 Araromi ta Garin Badin

Gobara ta kone shaguna 45 Araromi ta Garin Badin

Rahotanin daga jihar Oyo dake kudancin Nijeriya sun tabbatar da kunewar kasuwar Araromi dake garin Badin a dare asabar.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tace wutar ta kama da misalin karfe 2 na dare inda ta kone shaguna 45 kurmus a kasuwar dake matsayin babba kasuwa a birnin Badin da ake sayar da sassa mota,
Da yake ganawa da manema labarai babban daraktan hukumar Rev. Canon Yemi Akinyinka a ranar asabar, yace jami’an hukumar sun sami nasarar kashe wutar da misalign 5 na safiyar Asabar.
“jami’an mu na kofar shiga kasuwar ta Agodi tun karfe 2:30 na dare, suna cigaba da dakile wutar don ganin bata lakume dokiya mai yawa ba.
“bazan iya fadin ainihin adadin shagunan da suka kone ba, kun san abu ne yazo fuji’a, kuma y afara tsakar dare. Amma dai akalla shaguna 45 sun kone.
Wannan na zuwa ne makwanni bayan wata motar tanka ta kwace a garin na badin abinda ya haifar da asara mai tarin yawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp